Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Yiwa Wasu 'Yan Majalisar Nasarawa Barazanar Tsigesu


Gwamna Tanko Al-Makura na Jihar Nassarawa wanda yake fuskantar barazanar tsigewa daga majalisar dokokin jiharsa

Yayin da 'yan majalisar dokokin jihar Nasarawa ke yiwa gwamnansu barazanar tsigeshi al'ummar wasu kananan hukumomi suna yiwa wasu 'yan majalisar barazanar tsigesu.

Karamar hukumar Obi na cikin daya daga cikin kananan hukumomin da suke neman tsige 'yan majalisunsu.

A karamar hukumar Obi 'yan jam'iyyar APC na neman dan majalisa mai wakiltar yankunan Adudu, Obi, Tudun Adabu, Agwatashi da Dedere, Muhammed Sidi Bako kan ya dawo gida domin su ma su tsigeshi. Alhaji Abdullahi Anawo tsohon shugaban jam'iyyar CPC a yankin Dedere yace su suka zabi dan majalisar kuma yana yin abun da basu aikeshi yayi ba.

Kamata yayi dan majalisar ya nemi shawarar da majalisa ta tsayar daga wurinsu kana su bashi tasu shawarar abun da zai yi a madadinsu a majalisar. Ba zai yi gaban kansa ba yace zai tsige gwamna abun da basu aikeshi yayi ba. Idan ya dawo gida zasu tsigeshi.

To amma da yake dan majalisar Muhammed Sidi Bako yana jam'iyyar PDP ne 'yan jam'iyyar APC basu da hurumin cewa zasu dawo da shi domin su tsigeshi, inji jam'iyyar PDP.

Ali Idris Adudu shugaban PDP a yankin yace zanga-zangar da wasu 'yan jam'iyyar APC suka yi a mazabar Sidi Bako sun yi kuskure domin basu ne suka zabeshi ba. Su 'yan PDP suka zabeshi kimanin shekara bakwai ke nan kuma suna jin dadin aikin da ya keyi, ya kuma cigaba da aikin.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00
Shiga Kai Tsaye

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG