Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zaben Sarki Oni na Ife


FILE

Hukumomi a Jihar Osun da masarautar Ife suna ci gaba da aikin zabe da nada sabon sarki bayan rusuwar Oni na Ife Oba Sijuwade.

Ana haka ne kuma wata tawagar wakilan Majalisar Dittijai ta je jihar domin mika ta’aziyyar mutuwar basaraken.

Sanata Abdullahi Adamu ne ya jagoranci tawagar ‘yan majalisar, yace “duk wanda ya san marigayin, ya san cewa yana da mutunci, daraja, gaskiya da rawar da ya taka wajen hada kan Najeriya. Mutum ne baya harshen damo.”

Shi kuwa Sakataren gwamnatin Jihar Osun Alhaji Mashood Adeyoti da yayi wa Sanatocin maraba lale ya bukaci shuwagabannin da su ajje ban-bance ban-bancensu a gefe su yiwa kasar aiki don a sami cigaba.

Shugaban majalisar dokokin Jihar Osun Najim Salam yace wannan ziyarar ta’aziyyar ta nuna hadin kan Najeriya.

“Hadin kan Hausawa da Yarabawa zai karfafa hadin kan kasar nan, kuma wannan zai nuna ma duniya cewa kan mu a hade yake” a cewar Mr. Salam.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG