Accessibility links

Yau Lahadi miliyoyin yan kasar Mexico suke zaben shugaban kasa.

Yau Lahadi miliyoyin yan kasar Mexico suke zaben shugaban kasa.

Kididdiga ta nuna cewa Enrique Pena Bieto dan takarar jam’iyar Institutional Revolutionary ko PRI a takaice ya doshi samun gagarumar nasara.

Tun shekara ta dubu biyu jam’iyar PRI ke jan ragamar mulkin kasar Mexico cikin zargin cin hanci da rashawa da magudin zabe da kuma danniya da Mario Vargas Losa wanda ya taba samun lambar yabo ta Nobel ta taba baiyanawa a zaman mulkin danniya tsagoranta.

Dan takara na biyu wajen farin jinni shine Andres Manuel Lopez Obrador wanda ya sha kaye a zaben da aka yi a shekara ta dubu biyu da shida. Ta uku kuma, itace ‘yar takarar jam’iyar PAN, Josefina Vazquez Mota, wadda itace mace farko a kasar data taba takarar shugabar kasa.

A ranar Alhamis yan takarar guda uku suka rattaba hannu akan wata yarjejeniyar da suka yi alkawarin mutunta ko kuma yin na’am da sakamakon zaben na yau Lahadi. Haka kuma yarjejeniyar ta tanadi suma yan kasar su mutunta sakamakon zaben duk da sabanin ra’ayin siyasa.

An dai fara zaben zaben da misalin karfe takwas na safe agogon can, kuma ana sa ran yin sa’o’i goma sha biyu ana zabe kafin a rufe rumfunan zabe.

XS
SM
MD
LG