A yau Lahadi, al'umar Ukraine sun dunguma zuwa rumfunan zabe, domin kada kuri'unsu a wani zaben 'yan majalisu na gaggawa, wanda sakamakonsa zai kara jaddada zaben sabon shugaban kasar da aka yi.
A watan Afrilun da ya gabata, wani gagurumin goyon baya da aka nunawa Volodymyr Zelenskiy ta ba shi damar darewa karagar mulkin kasar.
Zelenskiy, ya kasance mai wasan barkwanci, wanda ke yawan fitowa a matsayin shugaban kasa a wasannin kwaikwayon da yake yi.
Ana sa ran jam'iyyar sabon shugaban kasar ta taka rawar gani a wannan zabi, inda akasin hakan zai tilasta mata kafa gwamnatin hadaka.
Masu fashin baki na cewa, mai yiwuwa wannan majalisa ta iya zama banbarakwai, lura da cewa kashi 70 cikin 100 na adadin mambobinta duk sabbi ne.