Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana zaman dar dar a Masar


Wani dan kasar Masar
Wani dan kasar Masar

Ana zaman dar dar a kasar Masar, a yayinda jami’an kasar ke shirye shiryen baiyana sakamakon zaben fidda gwani a aka yi a kasar wanda ake rikici akansa.

Ana zaman dar dar a kasar Masar, a yayinda jami’an kasar ke shirye shiryen baiyana sakamakon zaben fidda gwani a aka yi a kasar wanda ake rikici akansa.

Yay asabar baban sakataren hukumar zaben kasar Matem Bagato ya fada cewa gobe Lahadi idan Allah ya kaimu da misali karfe uku na yamma agogon Masar, shugaban hukumar zabe Faruk Sultan zai bada sanarwar sakamakon zaben.

Dukkan yan takarar, dana kungiyar Muslim Brotherhood Mohammed Morsi da kuma tsohon Prime Ministan kasar Ahmed Shafiq, kowane ya ayyana cewa shine ya zama zakara, a zaben dake neman maye gurbin tsohon shugaba Hosni Mubarak wanda aka tilastawa yin murabus a bara.

Tunda farko a shirya bada sakamakon zaben a ranar Alhamis, to amma hukumar zaben kasar tace tana bukatar karin lokaci domin tayi bincike akan zarge zargen da dukkan yan takarar suka yi cewa an tupka magudi

XS
SM
MD
LG