Accessibility links

Ana Zaman Makoki Na Kwana Uku A Kasar Ivory Coast


Wani soja tsaye kusa da komotsan wadanda aka tattake a turmutsutsu
Kasar Ivory Coast ta fara zaman makoki na tsawon kwana uku jiya Laraba bayan turmutsutsun da ya yi sanadin mutuwar a kalla mutane 60 a jajibirin sabuwar shekara gabilinsu matasa.

An murkushe dama daga cikin mamatan ne ko aka matse su suka kasa lunfashi lokacin da lamarin ya faru a Abidjan ranar Talata.

Masu gudanar da bincike basu da tabbacin abinda ya haddasa turmutsutsun da ya faru kusa da wani babban filin wasa inda dubun dubatan mutane suka taru domin kallon wasan wuta.

A shekara ta dubu biyu da tara, turmutsutsu a wannan filin wasan ya yi sanadin mutuwar mutane 22.
XS
SM
MD
LG