Accessibility links

Ana Zaman Tankiya A Maiduguri

  • Garba Suleiman

'Yan bangan Fararen Hulan JTF suna anfani ne da kulake da sanduna da makaman da aka sarafa cikin gida suna sintiri a kan titunan Maiduguri, Najerya.

A bayan da dan sanda ya bindige ya kashe dan bangar farar hula daga cikin masu taimakawa jami'an tsaro wajen farautar 'yan Boko Haram

Ala'mura sun nemi sukurkucewa a garin Maiduguri, hedkwatar jihar Borno lahadi din nan, a bayan da wani dan sanda ya bindige ya kashe daya daga cikin matasa 'yan banga da ake kira "Civilian JTF" dake farautar 'yan Boko Haram.

Wannan lamarin ya faru ne da tsakar rana a yayin da mataimakin shugaban Najeriya, Namadi Sambo, da gwamna Shettima Kashim na Jihar Borno da kuma Sultan na Sokoto, Muhammad Saad Abubakar, suke kaddamar da aikin kwasar maniyyata aikin Hajjin bana a babban filin jirgin saman Maiduguri.

Wasu daga cikin matasan da suke wurin a lokacin da wannan abu ya faru, sun ce lamarin ya faru a lokacin da suka biyo ta hannun da ba nasu a kan hanya, bayan da suka kamo wani dan Boko Haram daga garin Benisheikh su na son kai shi wurin soja, dab da tashar motocin safa na Borno Express.

Wani dan sanda ya tare su yace su bi ta daya gefen hanyar, sai suka ce masa sun kamo dan Boko Haram ne ba zasu iya bi ta can ba, sai yayi barazanar bude musu wuta, sai wani daga cikin matasan ya kalubalance shi. Daga nan ne kafofi suka ce dan sandan ya bude wuta ya kashe daya daga cikinsu.

Matasan da suka fusata sun rufe wannan dan sanda da duka da sara da adduna, su na barazanar kashe shi, da kyar aka kwace shi. Ya zuwa yanzu babu tabbas a kan halin da wannan dan sanda ke ciki, sai dai an gan shi jina-jina ana kokarin cetonsa zuwa hedkwatar 'yan sanda.

Daga bisani matasan sun tare hanyar da gwamna da mataimakin shugaban suka bi daga filin jirgin sama, inda suka kona tayu a kan hanyar motar Maiduguri zuwa Kano.

Gwamnan na Jihar Borno, ya bayyana jimamin wannan lamarin, ya kuma yi alkawarin biyan diyyar Naira miliyan 3 da rabi ga iyalan matashin da aka kashe. Har ila yau, yayi musu alkawarin gidan zama.

Wakilin Sashen Hausa, Haruna Dauda Biu, ya aiko da karin bayani daga Maiduguri.
XS
SM
MD
LG