Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Tsaro A pakistan Suna Fuskantar Zargin Kasa Hana Kai Hare-Haren Ta'addanci.


Mazauna birnin Quetta suke duba baraguzan gine gine da harin bam a wata kasuwa ya rusa ranar Asabar.
Gwamnan lardin Baluchistan yana caccakar jami’an tsaron kasar saboda kasa hana kai harin da aka kai jiya Asabar wanda aya kashe akalla mutane 80, ya jikkata wasu fiye da dari.

Gwamnan lardi Zulfiqar Magsi ya fada yau lahadi cewa kodashike an sakarwa jami’an tsaron kasar mara kan yadda suke gudanar aiki kan kungiyoyin masu tsatstsaran ra’ayi, sun gaza ganowa da wargaza irin wannan hari da aka kai jiya Asabar a wata kasuwa da take cike makil da mutane.

Haka ma masu zanga zanga sun cika titunan birnin na Quetta, da Karachi dake kudancin kasar, harda Islamabad babban birnin kasar, suna neman da gwamnati ta dauki mataki.

Fashewar wacce ta auku babban birnin lardin Quetta an auna shi kan ‘yan tsiraru da ake kira Hazara, wadanda ‘yan shi’a ne da suka zauna a lardin Baluchistan bayan sun kaura daga Afghanistan fiye da shekaru dari da suka wuce.

Kungiyar mayakan sakai da ake kira Lashkar e-Jaghvi ta sdauki alhakin kai harin da ma wani da aka cikin watan jiya wanda ya halaka mutane 90.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG