Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zargin Shafukan Sada Zumunta da Gurbata Halayyar Matasa


Facebook

Tun lokacin da shafukan sada zumunta, walau Facebook ko Twitter, suka fito suka samu karbuwa a duk fadin duniya saboda saukin samun labarai da jin wakokin da dai sauransu ba tare da wata shamaki ba

To sai dai rashin shamakin ko takunkumi ya jefa iyaye da shugabannin addini a Najeriya cikin ayar tambaya gameda alfanu ko illar yin anfani da shafukan a tsakanin matasa. Tambayar ko ta taso ne saboda zargin gurbacewar halayyar matasan, musamman wasu dabi’un maza da mata.

Twitter
Twitter

Ana kuma zargin matasan da kallon wasu finafinan batsa.

Malam Umar Faruk Abdullahi wani uba ne dake kuka gameda yin anfani da shafukan na zamani tsakanin matasa. Y ace yin anfani da Facebook ko Twitter ta zama hanyar bata yara mata kanana da bata samari da kallon finafinan batsa da makamantansu saboda haka ya kira iyaye su tsare su kuma kula da ‘ya’yansu daga abubuwan dake faruwa.

Wani matashi dake anfani da shafukan y ace komi aka yi yana da mahimmanci da kuma illarsa. Y ace an yisu ne domin sada zumunci amma kuma idan wasu suna anfani dasu ta hanyar da bata dace ba sai a yi hattara. Ya kara da cewa kowa ya tuna cewa duk abun da mutum yayi ya yiwa kansa ne. Ya kira matasa su kiyaye yadda suke anfani da kafofin.

Sai dai masana na ganin alfanun amfani da shafukan ya fi illarsu. Dr. Shu’aibu Shehu mai sharhi kan harkokin yau da kullum yace gudummawar da kafofin sadarwa suke bayarwa wajen bunkasa bincike ba zai misaltu ba.

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG