Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anyi Zanga-Zangar Rashin Wadataccen Ruwa A Birnin Isfahan


Iran - Water shortage Chaharmahal va Bakhtiari
Iran - Water shortage Chaharmahal va Bakhtiari

An gudanar da zangar-zangar rashin wadataccen ruwa a birnin Isfahan, Birni na ukku mafi girma a Iran

Mahukunta a kasar Iran sun fara murkushe masu zanga-zangar adawa da karancin ruwa a birnin Isfahan birni na ukku mafi girma a kasar.

A sanarwan da aka nuna ta kafar sadarwa ta Zamani wanda sashen harshen Fashiya na wannan gidan Radiyon ya kalla, ana jin karan harbin bindigar ‘yan sanda a gabashin birnin na Isfahan ajiya asabar, kana ko baya ga harbin ana jin ‘yan sanda na cewa wannan gangamin naku fa ya sabawa doka.

Kawo jiya asabar an shiga kwanaki biyar Kenan ana fama da karancin ruwa a wannan birnin.

Sai dai Videon na jiya asabar shine karon farko da aka ga ‘yan sanda na kokari tarwatsa masu zanga-zangar.

Daya daga cikin shugabanin kasar, Ayotollah Yousef Tabatabaye Nejad ya gargadi masu zanga-zangar,yace suna kokarin tayarda husuma ne kawai don haka su bari.

Wannan zanga-zangar dai ba shine na farko ba domin ko ya samo asali ne tun lokacin da manoma a gundumar Isfahan dake garin Varzaneh sune suka fara shi ganin sun fara fuskantar karancin ruwa tun a cikin watan Fabarairu lokacin da aka karkata ruwan da ake basu zuwa masanaantu a makwabciyar gundumar Yazd, wannan ya haifar da fito na fito da masu zanga-zanga da jamiaan tsaro.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG