Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC Ta Karyata Zargin Shirin Tube Sarkin Musulmi


Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar (ii)
Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar (ii)

Yayin da yakin neman zabe ke dada tsanani a Najeriya, an shiga yada labarai ko jita-jita da zummar yin illa ga abokan karawa. Watakila irin wannan al'amari ne ke neman girgiza jahar Sakkwato, inda aka ce wai kujerar Mai Alfarma za ta yi rawa.

Yayin da ake ta yada jita-jita ta kafafen sada zumunta cewa jam’iyyar APC na wani kulle-kullen tube Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar Na Biyu daga sarauta muddun jam’iyyar ta APC ta ci zaben gwamnan jahar, jam’iyyar ta APC ta ce wannan zargi da ake ma ta na shirin abin da ake kira, “Sabon Gwamna, Sabon Sarki,” ba gaskiya ba ne. Ta ce an kago ne da zummar sa Mai Alfarma da sauran jama’a su ga bakin APC.

Sakataren Jam’iyyar PDP a jahar ta Sakkwato Alhaji Kabiru Aliyu ya ce shirin APC na Sabon Gwamna, Sabon Sarki gaskiya. Ya ce ko a harabar Fadar Mai Alfarma ‘yan APC sun sha cin mutuncin Mai Alfarma ta wajen fadin cewa za a yi Sabon Gwamna, Sabon Sarki.

To amma a martaninta, jam’iyyar APC mai adawa a jahar, wadda amma ta yi galaba a zaben Shugaban kasa a jahar, ta karyata wannan zance ta bakin shugabanta na jahar, Alhaji Isa Sadik Achida, wanda ya ce jam’iyyar APC ta na mutunta Mai Alfarma da sarautar Sarkin Musulmi da kuma gidan sarautar baki daya. Ya ce hasali ma ba su da wata niyya ta yi ma wani bita-da-kullin siyasa. Jam’iyyar ta APC ta ce wasu jiga-jigan ‘yan PDP, ciki har da shugaban PDP a jahar, Ibrahim Mil Goma da tunzura jama’a, zargin da ita ma PDP ta ce kazafin siyasa ne kawai.

Ga dai Murtara Faruk Sanyinna da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG