Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC ta Zargi Gwamnatin Jigawa Akan Kananan Hukumomi


APC
APC

Jam'iyyar adawa ta APC ta zargi gwamnatin jihar Jigawa da mayarda kananan hukumomi tamkar wani bangare ne na ofishin gwamnan.

Nasiru Garba Dantiye daya daga cikin shugabannin jam'iyyar APC a jihar yace babu wani shugaban karamar hukuma da zai ce ana bashi kudinsa ya je yayi ayyukan da suka cancanta. Ba abun da mutane suke bukata ba za'a yi masu sai yadda gwamnati ta gani kuma tana son ta yi. Saboda haka a jihar jigawa babu wata karamar hukuma dake kashe kudinta bisa ga tsarin mulkin kasa.

Idan ba'a manta ba kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi ta dade tana kuka kan abun da tace ya hana ruwa gudu a kananan hukumomin kasa Najeriya. Kungiyar tace gwamnoni na yiwa kananan hukumomi shishshigi a harkokin kashe kudadensu.

Shugaban kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi kasa baki daya Ibrahim Khalil yace tun shekarar 1999 da aka fara dimokradiya suka gano akwai gibi akan tsarin kananan hukumomi. Yace shi mutumin karkara gwamnoni basu daukeshi komi ba.

To amma Alhaji Salisu Sale Indirawa kwamishanan kananan hukumomin jihar Jigawa ya musanta zargi da APC tayi da kuma fahimtar ma'aikatan kananan hukumomin ta kasa. Yace a jihar Jigawa shugabannin kananan hukumomi suna cin gashin kansu. Yace da kwamishanan kudi ya karbo kudin jijhar za'a ware na kananan hukumomi a aika masu cikin asusunsu kai tsaye. Da zarar an tura masu kudinsu to ya rage garesu su yi tunanin abun da jama'arsu ke so. Kowace shekara kananan hukumomi suna yin kasafin kudi akan bukatun jama'arsu.

Ga rahoton Mahmud Kwari.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG