Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC Ta Zargi Gwamnatin Taraba da Yin Mulkin Danniya


Sanata A'ishah Jummai Alhassanta jam'iyyar APC kuma 'yar takarar gwamnan jihar dake shari'a da gwamnan akan sakamakon zabe

A wajen taron manema labarai shugaban jam'iyyar APC ya zargi gwamnatin Taraba da yin mulkin danniya da kama karya da hana jama'a fadin ra'ayoyinsu.

Alhaji Hassan Jika Ardo shugaban jam'iyyar APC a jihar Taraba ya zargi gwamnan jihar da yin kama karya tare da bada misali wai ana muzgunawa wasu ma'aikata a jihar da kuma sauya masu wuraren aiki sakamakon zuwansu kotu domin sauraren shari'ar da ake yi akan kujerar gwamnan.

Haka ma yace ana yiwa wasu ma'aikatan gidan rediyon jihar bisa zargin cewa suna caccakar manufar sabuwar gwamnatin a dandalin zumunta na Facebook.

Akwai kuma korar wani tsohon dan jarida kuma tsohon hadimin tsohon mukaddashin gwamnan jihar Alhaji Garba Umar, wato Aaron Atimas da gwamnan ya yi. Bugu da kari gwamnatin jihar ta kuma fitar dashi daga cikin gidan gwamnatin da yake haya yau fiye da shekaru goma sha biyar alatilas.

Alhaji Ardo yace mutane su lura da kyau. Abun da suke fadi ya faru ne a zahiri. Yace misali a jihar mutum bashi da 'yancin ya fadi ra'ayin kansa ko ya zabi abun da yake so. An sake wa mutane wuraren aiki saboda fadin ra'ayoyinsu.

Shi ma Mr. Aaron Atimas yace gwamnatin ta bashi wa'adin ficewa cikin gaggawa daka gidan da yake yanzu. Yace a wurin da yake zaune su da suka bar aiki sun fi goma amma ba'a taba sauran ba sai shi. Akwai wasu kuma a wasu gidajen amma ba'a yi masu ba sai shi kadai. Yace da sassafe aka je gidansa da misalin karfe biyar domin bashi takardar fita daga gidan. Yace mulkin danniya ke nan ba na dimokradiya ba.

A martanin da ya bayar gwamnan jihar ta bakin mai bashi shawara ta fuskar harkokin siyasa Alhaji Abubakar Bawa ya musanta zargin. Yace a matsayinsu na gwamnati ko an yiwa wani canjin wurin aiki ko menene ma basu sani ba. Dangane da fitar da Mr. Atimas daga gidansa sai yace basu san da batun ba kuma watakila maganar tsakninsa ne da masu kula da gidajen.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:59 0:00

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG