Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Arangama Tsakanin Bata-Gari A Wata Kasuwa Tare Da Kone Shaguna Ya Janyo Kama Mutane 50 A Legas


'Yan sanda Najeriya yayin wani atisaye da suka yi a Abuja (Hoto: Facebook/Rundunar 'Yan sandan Najeriya - Wannan tsohon hoto ne)
'Yan sanda Najeriya yayin wani atisaye da suka yi a Abuja (Hoto: Facebook/Rundunar 'Yan sandan Najeriya - Wannan tsohon hoto ne)

A yau Alhamis, jami’an Rundunar ‘Yan Sandan Legas, suka kama wasu mutane 50 dangane da arangamar wasu bata-gari a shahararriyar kasuwar kayan abincin nan ta Ile-Epo dake karamar hukumar Alimosho ta jihar.

Hatsaniyar da ta samo asali a daren jiya Laraba ta cigaba har zuwa wayewar garin Alhamis a yayin da bangarorin bata-garin 2 ke kokarin daukar fansa game da wani al’amari da ba’a bayyana ba.

A yayin hatsaniyar ne bata-garin suka cinnawa wasu shaguna makare da kayan abinci wuta.

Tuni dai aka tura ayarin farko na masu kai dauki da suka hada da jami’an ‘yan sanda dana kwana-kwana zuwa wajen da al’amarin ya faru.

Sai dai a cikin wata sanarwa, Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin, yace zaman lafiya ya dawo a kasuwar.

Yace “An kama fiye da mutane 50 da ake zargi da hannu a lamarin sannan an lalata gidajen wucin gadin da suke zaune a ciki, don haka an tarwatsa su yadda ya dace”.

“Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Legas, Adegoke Fayoade, ya bada umarnin gaggauta gurfanar da bata-garin gaban kotu, sannan yayi gargadin cewar rundunar za ta sanya kafar wando daya da duk wanda aka samu yana kokarin tada zaune tsaye, kamar yadda doka ta tanadar”, a cewarsa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG