Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AREWA A YAU: Tinubu Ya Sha Alwashin Kawo Karshen Barace-Barace A Arewacin Najeriya - Nuwamba 29, 2023


Nasiru Adamu El-Hiyaka Lokacin Kan Hanyar Kaduna Zuwa Abuja
Nasiru Adamu El-Hiyaka Lokacin Kan Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

Sabon shirin AREWA A YAU zai tabo alwashin mai taimaka wa shugaba Tinubu kan lamuran nakasassu Komred Muhammad Abba Isa, na janye masu bara daga kan tituna da ma dawo da masu nakasa na arewa da su ka shige jihohin kudancin Najeriya.

Daga nan shirin zai koma kan zantawar nan da masanin kididdiga Farfesa Sadik Umar Abubakar kan yanda a ka samu matsalolin da ke haifar da kuncin rayuwa a arewa.

Kwanannan ministar jinkai Betta Edu ta bayyana cewa kashi 10% na tallafi ga marar sa galihu zai tafi ne ga masu bukata ta musamman.

Mai taimaka wa shugaba Tinubu kan nakasassun Komred Muhammad Abba Isa ya ce ya na jin takaicin yanda ya ke mai nakasa ya ga 'yan uwan sa na galabaita.

Masanin kididdiga Farfesa Saik Umar Abubakar da a farkon zantawa ya dora alhakin karancin kudin shiga ga watsi da kananan sana'o'i, ya cigaba da bayanin hanyoyin har ma da yanda za a samu gyara.

Saurari shirin:

AREWA A YAU
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:09:41 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG