Ana wata ga wata, ayayin da wasu kasashe a duniya ke bukatar a samar musu da na’urar kwamfuta me kwakwalwa, a makarantuni don inganta ilimi dama shiga cikin daidaito da sauran kashashe a duniya, don inganta tattalin arzikin kasa da wayar da kan al’umah.
Sai gashi a nan kasar Amurika, kwanaki kadan bayan wani jawabi da shugaban kasar Amurika Barak Obama, yayi na cewar za’a samar da Karin yawan kwamfutoci a azuzuwan yara da kuma samar da yanar gizo a kyauta ga ‘yan makarantar primary da sakandire a nan amurika. Ana cikin haka sai ga wasu tarin farfesoshi suna ganin wannan ba’abu ne da yadace da ‘yara ba, acewar daya daga cikin wadannan farfesoshin me suna Sunan Pinker, tace ai idan aka duba yara da suke da kwanfuta da yanar gizo aka hadasu da abokansu yara wadanda basu da yanar gizo, to za’a ga cewar hazakar su ba daya take ba. Don haka suna ganin wannan kawai salo ne wanda zai bata ingancin karatun yara a wadannan matakin na primary da sakandire.
Kuma sun yi nuni da cewar duk iyaye yakamata su maida hankali akan irin abubuwan da 'yayansu keyi a kan kwanfuta mai kwakwalwa idan har suna da yanar gizo. Don sunce wani bincike da aka gudanar yanuna cewar, yara na amfani da wadannan na'urorin wajen wasu bincike da basu da alaka da inganta ilimi, hasalima suna ganin wannan wata damace wada yara zasu lalace idan ba'a duba abubuwan da sukeyi akai akai.