Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Australia Ta Bada Sanarwar Dakatar da Kai Hare-haren Sama cikin Syria


Jiragen yakin Australia
Jiragen yakin Australia

Biyo bayan musayar yawu tsakanin Rasha da Amurka sanadiyar harbo jirgin saman yakin Syria da Amurka tayi, yanzu Australia ta dakatar da kai hari ta sama kan Syria.

Australia ta bayarda sanarwar a yau Talata cewar zata dakatar da hare-haren da mayakanta na sama suke kaiwa a tsakiyar Syria na wani lokaci.

Wannan matakin yana zuwa kwanaki kadan a bayan da wani jirgin saman yakin Amurka ya harbo wani jirgin saman yakin Syria, abinda ya sa kawar Syria din, watau Rasha, tace daga yanzu zata dauki duk wani jirgin saman yaki na kasashen kawancenda Amurka take jagoranta a zaman na abokan gaba a samaniyar Syria.

Australia tana cikin kasashen kawancen da suka fara kai hare-hare daga sama a kan mayakan Daesh ko ISIS cikin kasar Syria a watan Satumbar 2014.

Wata sanarwa daga ma'aikatar tsaron Australia ta ce zata nazarci yanayin samaniyar Syria ta kuma yanke shawara a kan abinda zata yi nan gaba. Australia ta ce zata ci gaba da kai hare-hare ta sama a makwafciyar Syria, Iraq.

Jiya Litinin Amurka ta mayarda martini da kakkausan harshe ga wannan barazana ta Rasha.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG