Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Australia Ta Kama Dan Korea Ta Arewa Yana Yi Mata Leken Asiri


Shugaban kasar Korea ta Arewa, Kim Jong Un

Jami'an tsaro a kasar Australia sun kama wani haifaffen dan kasar Korea ta Arewa da suke zargi da gudanar da ayyukan leken asiri.

Jami'ai a Australia sun ce sun kama wani haifaffen dan kasar Korea ta Arewa a matsayin wakilin kasar mai leken asiri da ke da alaka da tattalin arzikin kasa.

A jiya Asabar ne dai jami'an kasar ta Australia suka kame Chan Han Choi wanda ya zama dan kasar ta Australia shekaru da dama, kuma yana zaune ne a ciki kasar .

‘Yan sandan kasar suka ce da Choi ya yi nasarar aiwatar da mummunar kasuwancin da ya yi niyyar yi wanda ya hada da sayar da makaman kare dangi, da ya mallaki na miliyoyin daloli a madadin kasar ta Korea ta Arewa.

Kamar yadda babban jami'in ‘yan sandan na kasar ta Australia Neil Gaughan ke cewa, wannan abu ne da ba su taba gani ba a kasar Australia.

Gaughan ya ce kuma bincike ya tabbatar musu da cewa Choi yana da alaka da manya-manyan jami'an gwamnatin kasar Korea ta arewa.

Babban jami'in ‘yan sandan ya ce ba shakka Choi mutun ne da ke biyayya ga kasar ta Korea ta Arewa, domin ko bincike ya nuna musu cewa akwai wani ra'ayi na manya-manyan kasar ta Korea ta Arewa da yake karewa.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG