Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Duniya

Australia Za Ta Raba Wa Mutane Kudin Tallafi Domin COVID-19


Frai minista Scott Morrison

Yayin da ake samun hauhawar adadin masu kamuwa da cutar coronavirus a Australia, gwamnatin kasar ta bada sanarwar tanada kudin tallafi.

Hakan na zuwa ne yayin da ake samun karuwar rashin aikin yi a kasar.

A yau Alhamis, Firai Minista Scott Morrison ya sanar cewa gwamnatinsa za ta kashe karin dalar Amurka biliyan daya a wani shirin tada komadar ma’aikata, inda za a biya rabin albashin masu koyon aiki karkashin masu kananan sana’o’i.

Za a kuma yi amfani da sauran miliyan 400 wajen horar da ma’aikatan wasu sabbin dabarun da za su yi tasiri wajen farfado da tattalin arzikin kasar bayan annobar ta kau.

Australiya na da wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 kusan dubu goma sha daya, a cewar cibiyar bin didigin cutar coronavirus ta jami’ar Johns Hopkins.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG