Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Azerbaijan Ta kaddamar Da Binciken Harin 'Yan Ta'adda


Yuta ştatının Brigham Young Universitetində Azərbaycan nümayəndə heyətinin üzvləri ilə görüş keçirilib, 2 mart, 2023.
Yuta ştatının Brigham Young Universitetində Azərbaycan nümayəndə heyətinin üzvləri ilə görüş keçirilib, 2 mart, 2023.

Hukumar tsaron farin kaya ta Azerbaijan ta fada a yau Laraba cewa, tana gudanar da bincike kan "wani harin ta’addanci”, bayan da aka harbi wani dan majalisar dokoki mai tsattsauran ra’ayin kin jinin Iran, aka kuma yi masa rauni a gidansa. 

Hukumar tsaron ta fada a wata sanarwa cewa, an kwantar da dan majalisar, Fazil Mustafa a asibiti, sakamakon raunin da ya samu a kafadarsa da cinyar kafarsa, sa’adda aka harbe shi da bindiga a jiya Talata.

Sanarwar ta ce rayuwar sa ba ta cikin wani babban hatsari, yayin da kuma aka bude wani binciken aikata babban laifi, domin gano wadanda suka aikata lamarin.

Shafin yanar gizo na kafar yada labaran Azeri news, ya ruwaito Mustafa mai shekaru 57, yana fada a lokacin da yake a asibiti, cewa, an harbe shi da harsasai 2, yayin da yake tuka mota zuwa shiga garejin gidansa.

Hukumar tsaron kasar ta fada a sanarawar da ta fitar cewa, Mustafa yayi suna sosai akan tsattsauran ra’ayinsa kan Iran, makwabciyar Azerbaijan daga kudu.

XS
SM
MD
LG