Accessibility links

AZUMI: Shin Me Ya Sa 'Yan Kasuwa Ke Tsawala Farashin Kayan Masarufi


Lokacin azumi wani yana karanta Kur'ani Mai Girma cikin Masallaci

Kowacce shekara lokacin da jama'ar Musulmai ke shirin fara azumi akan samu hawa-hawar tashin farashin kayan abinci da na masarufi da na 'ya'yan iatace.

Yayinda hankalin jama'a ya koma kan shirye-shiryen fara daukar azumi a watan Ramadan su ma 'yan kasuwa suna kasawa da kuma tsawala farashin kayan masarufi.

Kama daga kayan abinci irinsu shinkafa, taliya da sukari da madara da kayan miya da man girki da kayan marmari irinsu 'ya'yan itatuwa da dai makamantansu farashinsu kan yi tashin goron zabi. Wani lokacin ma farashin na wuce hankali da kuma masu karamin karfi.

Malam Aminu Yahaya wani mai sayayya ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda 'yan kasuwa ke tsawala farashin kaya a watan Ramadan. Mutane sun dauki watan azumi wani wata ne mai daraja da albarka ga duka Musulmi saboda haka abubuwa sukan canza. Misali wadanda suke sayar da kayan abinci da na masarufi burinsu ne su samu riba kafin lokacin sallah. Duk abun masarufi su kan samu karin farashi.

Malam Yahaya Sokoto mai sayarda kayan marmari yana da nashi ra'ayin daban. Yace karin farashi ya danganta ga mutane. Wasu suna ganin idan azumi ya zo to lokaci ne da zasu nemi riba da dama. Dalili ke nan wasu suke kara kudi. Wani lokacin kuma tsadar mai ka iya haifar da tashin farashin kaya. Idan kuma ruwan sama ya yi yawa manyan motoci basa iya zuwa daukan kayan gona a kayuka domin sai su kafe. Sai dai a yi anfani da kananan motoci lamarin da kan kara farashen kaya.

Ga rahoton Babagida Jibrin.

XS
SM
MD
LG