Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba a sami ci gaba ba a tattaunawar Amurka da Rasha kan rikicin kasar Siriya


Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton,
Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton,
Babbar jami’ar diplomasiyar Amurka tace haka bata cimma ruwa ba a tattaunawar da ake yi da shugabannin kasar Rasha dangane da batun kasar Siriya.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta bayyana wajen taron kulin da ake gudanarwa a Rasha na kasashen dake kewayen tekun fasific yau lahadi cewa, ba a sami wata ci gaba ba a tattaunawarta da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da kuma ministan harkokin kasashen wajen kasar Sergei Lavrov kan matakan da za a dauka dangane da zanga zangar kin jinin mulkin kama karya na shugaba Bashar al-Assad.

Clinton ta ce idan suka ci gaba da fuskantar banbancin ra’ayoyi, zata yi aiki tare da kasashen da ra’ayinsu ya zo daidai wajen goyon bayan ‘yan mahayyar kasar Siriya a gwaggwarmayarsu.
XS
SM
MD
LG