Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Dokar Tsarin Mulki Ne Matsalar Nigeria Ba


ADAMAWA: PDM da aka sani da Atiku Abubakar tayi taro
ADAMAWA: PDM da aka sani da Atiku Abubakar tayi taro

Farfesa Ango Abdullahi Tsohon mai baiwa shugaban Nigeria Chief Olusegun Obasanjo shawara a harkokin noma yace lokaci yayi da 'yan Nigeria zasu dubi junan su su fada musu gaskiya.Yace a bar ganin lafin dokar kasa.Domin ba abinda ya samu dokokin Nigeria, illa masu sarrafa dokokin.

Tsohon mai baiwa tsohon shugaba Nigeria, Olusegun Obasanjo shawara a kan harakokin Noma Farfesa Ango Abdullahi yace matsalar Nigeria ba ta tsarin mulki kasa bace.

Farfesan yana maida martani ne akan kiran da shugabanni da gwamnati keyi na akai zuciya nesa game da tashe-tashen hankulan da kungiyar masu fafitikar kasar Biafra keyi.

Malamin na Jami’a yace asake duba al’amarin da idon basira domin ko ansha yiwa dokar kasa kwaskwarima amma har wa yau lamarin bai sake zani ba.

Yace muddin ba tsayawa akayi aka fadawa juna Gaskiya ba to har kullun za a koma ‘yar gidan jiya ne.

Shima da yake tofa albarkacin bakin sa game da wannan lamarin shugaban kungiyar nan da ake kira “Our Mumu Don Do”, Deji Yade Adeyanju yace sun goyi bayan bada belin Nnamdi Kanu ne da zummar cewa zaiyi fafitikar ganin an sama wa jama’ar yankin su ababen more rayuwa amma sai suka ga ya shiga wata sabga ta daban.

Ga Saleh Shehu Ashaka da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG