Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Tilas Sai An Kirkiro Kasar Falasdinu Ba -Jami'in Fadar White House


Kakakin Fadar White House
Kakakin Fadar White House

Wani babban jami'i a fadar white House ya fada jiya Talata cewa, sulhu ko zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinu, ba tilas sai an kirkiro da kasar Falasdinu ba, kuma dabara kai ga hakan- ya rage wa sassa biyun.

A tattaunawa da manema labarai gabannin ziyarar da Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu zai kawo nan birnin Washington DC Laraban nan, jami'in yace "Amurka ba zata tilasta sharuddan da za'a bi a cimma zaman lafiyan ba."

A hukumance, matsayar Amurka kan wannan batu itace, Isra'ila da Falasdinu su raba yankin gida biyu, inda watakil- yankin Falasdinu zai mallaki zirin Gaza, da kuma illahiri- ko wani bangare na yammacin kogin Jordan, da kuma gabashin birnin kudus wanda Falasdinawan suke son ya zama helkwatar kasarsu idan har ta kafu. Haka nan ma MDD tana goyon bayan kafa kasaer Falasdinu a zaman hanyar warware rikicin na gabas ta tsakiya.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG