Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Za Mu Cire wa China Kudaden Haraji Ba - Trump


Shugaba Trump yayin ziyarar da ya kai Ohio, Maris 20, 2019.

A cewar Trump, ana samun ci gaba a tattaunawar da ake yi da hukumomin Beijing, inda ya ce nan da wasu ‘yan kwanaki, wakilan Amurka za su tafi China domin ci gaba da tattaunawa

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce China za ta ci gaba da biyan kudaden harajin da aka saka mata nan da zuwa wani lokaci, ko da an cimma wata yarjeniyar kasuwanci.

A cewar Trump, ana samun ci gaba a tattaunawar da ake yi da hukumomin Beijing, inda ya ce nan da wasu ‘yan kwanaki, wakilan Amurka za su tafi China domin ci gaba da tattaunawar.

Sai dai masana tattalin arziki na ganin China ba za ta amince da matsayar ta Amurka ba.

Alkaluma dai sun nuna cewa, adadin kayayyakin da China take shiga da su Amurka, sun ninninka wadanda Amurkan take kai wa China.

Baya ga haka, wannan rashin daidaito a fannin kasuwanci a tsakanin kasashen biyu, shi ya dibi kashi 80 cikin 100 na adadin gibin da Amurka take samu a fannin kasuwancinta da kasashen duniya.

Facebook Forum

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG