Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Zan Kammala Wa’adin Mulki Na Na Biyu A Matsayin Shugaban Da Ya Gaza Ba - Buhari


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a lokacin da ya sauce a Najeriya.

Shugaban Najeriya Muhammafu Buhari ya lashi takobin cewa ba zai sauka daga kan kujerar shugabanacin kasar ba har sai ya kawo muhimman sauye-sauye da zasu kawo ci gaba.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a yayin ganawar sirri tsakaninsa da manyan hafsoshin tsaron kasar kamar yadda mai ba sa shawara kan kan sha’anin tsaron kasa, Birgediya Janar Babagana Monguno mai ritaya ya bayyanawa manema labarai a fadar shugaban bayan taron a ranar Alhamis.

Shugaban ya kuma dau alkawarin kawo karshen matsalolin tsaro da suka addabi kasar kafin karshen wa’adin mulkinsa na biyu da zai kare a watan Mayun shekarar 2023.

Haka kuma, a yarin ganawar ta sirri, ministan tsaro, Bashir Salihi Magashi da sauran manyan hafsoshin tsaron kasar sun mika rahoto game da yanayin da ake ciki a sha'anin tsaro a Najeriya.

Monguno, ya fadawa manewa labarai cewa shugaba Buhari ya yi marhabin da rahoton da aka mika masa game da yanayin tsaron kasar, musamman saboda nasarorin da aka samu a baya-baya nan na murkushe yan ta’adda a sassa daban-daban na Najeriya.

National Security Adviser, Babagana Monguno.
National Security Adviser, Babagana Monguno.

Haka kuma, Monguno ya bayyana cewa shugaba Buhari ya kuduri aniyyar kasancewar cikin shirin ko-ta-kwana domin gudanar da muhimman sauye-sauye don cimma nasarori ta fuskar tsaro da ma sauran fannoni a kasar.

Shugaban ya kuma ce a shirye ya ke ya yi wa tsarin tsaron kasar gyare-gyare idan bukatar hakan ta taso musamman a fagen yaki da yan ta’adda a Arewa maso gabashin kasar da ma sauran miyagun iri da suka addabi arewa maso yamma da sauran sassan kasar.

Idan ana iya tunawa, a baya-bayan nan rundunar sojin Najeriya ta kai farmaki a maboyar mayakan Boko Haram a dajin Sambisa da wasu wurare a jihar Borno da ta fi fama da hare-haren 'yan Boko Haram din.

Ana alakanta farmakin da rundunar sojin Najeriya ta kai kan maboyan mayakan Boko Haran da mika wuyan mambobin kungiyar ta mayakan inda wata sanarwar rundunar ta ce wasu mayakan sun tuba suna neman a yafe musu.

Idan ana iya tunawa, tun bayan labarin mutuwar shugaban mayakan Boko Haram, Abubakar Shekau, aka yi ta samun labarin cewa kungiyar ta shiga rudani.

Abubakar Shekau, Shugaban Kungiyar Boko Haram
Abubakar Shekau, Shugaban Kungiyar Boko Haram

Rahotanni dai sun bayyana cewa, Shekau ya tarwatsa kansa ne bayan da tsagin kungiyar mai mubaya'a ga kungiyar ISIS wato mambobin kungiyar ISWAP suka rutsa shi da wasu mataimakansa domin su yi wa ISWAP mubaya’a wanda ya ki ya ce ya gwammace ya mutu a kan ya mika wuya ga 'yan ISWAP.

Shugaba Buhari dai ya bayyana farin cikin sa ga nasarorin da aka samu a baya-bayan nan musamman sakamakon aikin sabbin manyan hafsoshin tsaron kasar.

A cewar Babagana Monguno, shugaba Buhari ya ce, a shirye yake ya yi karin sauye-sauye idan bai gamsu da aikin da ake yi ba kuma zai tabbatar da cewa an sami sauyi da ake bukata musamman ta fuskar tsaron al’ummar kasarsa.

XS
SM
MD
LG