Accessibility links

Babban Bankin Duniya Ya Yaba Harkokin Kasuwanci A Najeriya

  • Grace Alheri Abdu

Ministan Kudi a Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala, a wajen wani taron harkokin kudi

Babban bankin duniya ya yaba ci gaban da aka samu a fannin harkokin kasuwanci a Najeriya

Wani sabon rahoto da babban bankin duniya ya fitar ya yi nuni da cewa gwamnatin Najeriya ta dauki kwararan matakan bunkasa kananan masana’antu duk da yake matsalar wutar lantarki na ci gaba da kasancewa babbar kalubala a fannin tattalin arzikin kasar.

A cikin rahoton da bankin ya fitar, ya nuna cewa, tun a shekara ta dubu biyu da tara ne Najeriya ta fara aiwatar da tsare tsaren da suka taimaka wajen samar da yanayin da ke habaka kananan masana’antu da suka hada da samar da rance.

Rahoton yace Najeriya na daya daga cikin kasashe goma a duniya da aka sami ci gaba ainun a fannin samar da rance ga kananan masana’antu. Wakilin Sashen Hausa ladan Ibrahim Ayawa ya hada rahoto a kan wannan ci gaban
XS
SM
MD
LG