Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babbar Kasuwar Bernin Kebbi Ta Kone Kurmus.


Firemen try to extinguish a fire at Great Nigeria Insurance House in Lagos business district November 4, 2013. There have been no casualties reported, and the cause of the fire is as yet unknown. REUTERS/Akintunde Akinleye (NIGERIA - Tags: DI

Gobarar ta babbar kasuwar Birnin Kebbi babban birni jihar Kebbi ta soma ne tun da musalin karfe daya na dare inda ta dauki tsawon saoi da dama tana ci lamarin da ya shafi akasarin kasuwar baki daya.

Komred Sani Asha hura mai goro na cikin ‘yan kasuwar da wannan iftilain ya shafa.

‘’Ni kwance da daddare sai wani aboki na ya kira ni yace mani ga kasuwar mu ta kone da wuta musalin karfe 12;30, koda na zo abin yayi nisa kwarai, kwana-kwana sunyi iya bakin kokarin su amma lamarin yafi karfin su.Mutane sunzo domin su shigaamma jamiaan tsaro ko kuma masu gadin kasuwa su hana mmutane su shiga shi ya kawo jinkirin irin hasarar da akayi a cikin wannan kasuwa gaskiya da ace an bari an shiga tun farko da ba za ayi irin hasarar da akayi ba, masu gadin kasuwan sun hana mutane shiga ne domin kar ayi wa jamaa sata, amma da an samu shiga da hasarar ba zata kai haka ba duk da yake wasu sun tsira da wasu kayayyakin su.’’

To sai dai wakilin muryar Amurka, Murtala Faruk Sanyinna ya tambaye shi ko wane hali suke ciki yanzu ga kuma amsar da ya bashi.

‘’ALLAH kadai zai iya kawo saukin hasarar dukiyar da akayi domin batu na gaskiya kasuwar gaba ta kone domin cikin kashi 100 kashi 90 ya kone.’’

Wayewar garin gobarar tawagar gwamnatinjihar ta ziyarci kasuwar wadda take ci da wuta har lokain ziyarar jamiaan gwamnatin jihar.

Ga Murtala Faruk da ci gaban rahoton

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG