Accessibility links

Babbar jam'iyar hamayya a Koriya ta Kudu ta tsaida dan takararta na zaben shugaban kasa


Moon Jae-in yana gaida magoya bayansa
Babbar jam’iyar hamayya ta Koriya ta Kudu ta zabi dan takararta a zaben shugaban kasar da za a gudanar cikin watan Disamba.

Jami’yar Democratic United ta zabi tsohon lauyan kare hakkokin bil’adama kuma tsohon mai taimakawa shugaban kasa Moon Jae-in yau lahadi.

A jawabinsa na amincewa da tsaida shi takara, Moon ya yi alkawarin daukar matakan ganin an gudanar da taron koli da nufin tattaunawa da kuma kara hada kai da Koriya ta arewa a fannin tattalin arziki.

Dan takarar jam’iyar mai sassaucin ra’ayi, ya yi aiki a matsayin babban hafsan marigayi shugaba Roh Moo-hyun, wanda ya gudanar da taron koli da Koriya ta arewa a shekara ta dubu biyu da bakwai.

Moon zai tsaya takara da ‘yar takarar shugaban kasa ta jam’iya mai mulki Park Geun-hyu, ‘yar shugaban kasar dan mulkin kama karya da aka kashe, Park Shung-hee.

Binciken ra’ayoyin jama’a na nuni da cewa, Park ke kan gaba. Idan aka zabe ta zata kasance shugaban kasar Koriya ta Kudu mace ta farko.
XS
SM
MD
LG