Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babbar Jam'iyyar Hamayyar Uganda Na Shirin Kalubalantar Zaben Kasar


Kayayyakin Zabe A Kasar Uganda.

Babbar jam’iyar hamayyar kasar Uganda tana kokarin tara shaidun da zata kalubalanci sakamakon babban zaben da aka gudanar ranar goma sha takwas ga wannan watan na Fabarairu.

Dokar zabe ta kasar ta bada wa’adin kwanaki goma daga ranar da hukumar zabe ta sanar da sakamakon zabe, na kalubalantar sakamakon.

Shugaban jam’iyar Democratic Change (DFC) Mugisha Muntu yace jam’iyar tana iyaka kokarinta ta cika wa’adin, duk da abinda yace barazanar da suke ci gaba da fuskanta da tursasawa daga jami’an tsaro da ya hada da ‘yan sanda, dake neman gurguntar da yunkurin jam’iyar.

Mr Muntu yace wannan ya biyo bayan yawan kamawa da sakin Dr Kizza Besigye, FDC dan takarar shugaban kasar.

Yace shaidun farko sun nuna an murde sakamakon zaben wadansu mazabu. Yace sakamakon zaben da dukan jam’iyu suka rabbata hannu ya sha banban da wanda hukumar zabe ta sanar.

Kungiyoyin hamayya sun kuma zargi hukumar zabe da nuna wariya bayan zabe a yankunan da suke da karfi da ya hada da Kampala babban birnin kasar, inda aka fara zabe kimanin sa’oi bakwai bayan bude runfunan zabe a wuraren da jam’iyar National Resistance Movement (NRM) take da magoya baya.

Yace an fara zabe a wadannan mazabun a makare da gangan domin rage kuri’un ‘yan hamayya.

shugaban hukumar zabe Badru Kiggundu ya bayyana shugaba mai ci yanzu Yoweri Museveni a matsayin wanda ya lashe zaben da kashi sittin da digo bakwai cikin dari na kuri'un, yayinda Besigye yazo na biyu da kashi talain da biyar da digo uku bakwai cikin dari na kuri'un .

XS
SM
MD
LG