Accessibility links

Babu Belmokhtar Cikin Wadanda Harin Amurka Ya Kashe a Libya


Mayakan kungiyar al-Qaida a Libya

Kungiyar al-Qaida a Libya ta fitar da jerin sunayen wadanda harin Amurka a Libya aya kashe amma banda wanda suke nema ruwa a jallo.

Wata kungiya mai alaka da al-Qaida a Libiya ta fidda jerin wasu sunaye yau Talata na wadanda kungiyar tace sun mutu a hari ta sama da Amurka ta kai, amma bata sa sunan Mokhtar Belmokhtar ba a cikin sunayen, wanda shi ne muhimmin mutum wanda aka auna a harin.

Sanarwar ta Ansar al-Shariah ta musanta cewa akwai kuma wanda suka sutu bayan jerin sunayen.

Hare-haren boma-boman su ne na farko da Amurka ta kai ta sama a Libiya tun rikicin shekarar 2011 da aka yi wanda ya hambarar da dadadden shugaba Moammar Gadhafi. Jami’an Amurka dai basu tabbatar da mutuwar Belmokhtar ba, wanda shine jigo a kungiyar al-Qaida a yankin Mghreb kafin ya kafa tasa kungiyar ta ‘yan ta’adda mai suna Singers In Blood Battalion a shekarar 2012.

Amurka ta zargi Belmokhtar da laifin jagorantar harin da aka kai a wani ginin sarrafa iskar gas a shekarar 2013 a kasar Algeria wanda ya hallaka mutane 37, ciki har da amurkawa 3. Mahukuntan Amurka sun zargi Belmokhtar da laifufuka dake da nasaba da ta’addanci bayan harin bom din.

XS
SM
MD
LG