Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bakin Matasan Najeriya Ya Zo Daya Akan Haramtaciyar Kungiyar IPOB


Shugabannin Matasan Najeriya da suka tattauna a zauren Muryar Amurka dake Abuja kan IPOB da wakilin Muryar Amurka cikin farar riga a tsakiyarsu
Shugabannin Matasan Najeriya da suka tattauna a zauren Muryar Amurka dake Abuja kan IPOB da wakilin Muryar Amurka cikin farar riga a tsakiyarsu

A tattaunawar da suka yi a zauren taron Muryar Amurka dake Abuja, shugabannin matasan Yarbawa da na Igbo da na arewacin Naijeriya duk sun yi tur da kungiyar IPOB dake fafutikar neman kafa kasar Biafra ta hanyar hatsaniya da kwaranniya.

Muryar Amurka ta shirya taron tattaunawa na musamman da matasan Najeriya daga kabilu daban daban a zauren taronta dake Abuja babban birnin Najeriya a yunkurin neman bakin zaren warware rikicin da kasar ke fuskanta.

Chuks Nkem Onyaka daya daga cikin shugabannin matasan kabilar Igbo ya fara nashi jawabin ne da yabawa da haramta kungiyar IPOB ta 'yan aware da gwamnonin jihohin kudu maso gabas suka dauka. Ya na mai cewa basu da gaskiya saboda haka bai kamata a bari su cigaba da tada hankulan jama'ar kasar ba.

Shi ma Yarima Shettima shugaban hadakar kungiyoyin matasan arewa yana mai cewa sun gano manufar Nnamdi Kanu shugaban IPOB cewa so yake ya tada fitina da zara suka ga abun da ya fara aukuwa a Aba.Nan da nan suka tashi tsaye su ga cewa ba'a bar shi ya cigaba da tayar da kayar baya ba. Yace suna son zaman lafiya kuma kowa ya cigaba da zama inda yake lafiya ba tare da tsangwama ba.

Shi ma Aziz Olasumbo Saka shugaban kungiyar matasan Yarbawa ya aza laifin irin goyon bayan da Nnamdi Kanu ke samu kan rashin ayyukan yi. Yana mai cewa idan da suna da aikin yi ne ba zasu bishi ba . Aiki ne da babu ya sa suka zama karnukansa. Yana da abokanai a cikin kabilar Igbo kuma basa goyon bayan dan tawayen.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG