Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Balarabe Musa Ya Yi Allah Wadai Da Gidauniyar PDP Da na Sauran Jam'iyyu


Alamar PDP

Alhaji Balarabe Musa ya yi tir da yadda gwamnatocin siyasa a Nijeriya ya ce su kan kan dibi kudin jama'a su bai wa jam'iyyunsu su yi kampe.

Tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa, ya yi Allah wadai da gidauniyar da aka kafa wadda kowace gwamnatin jihar da PDP ke mulkinta ta ba da Naira Miliyan 50 don PDP ta yi yakin zabe da shi. Ya ce wannan kudin na jama’a ne da aka sata aka tara ma PDP don ta yi yakin zabe.

A hirarsu da abokiyar aikinmu Grace Alheri Abdu, Tsohon gwamnan ya ce abin takaici ne a ce wai akwai hukumomin yaki da rashawa da cin hanci irinsu EFCC da ICPC da Code of Conduct Bureau, wadanda ya kamata a ce tuni sun ce wani abu game da wadannan kudaden da kowace gwamnatin jiha ta PDP za ta bayar. Ya ce kowane dan Nijeriya ya san ba ma za a yi komai ba. Ya gwamnatocin PDP din ma ba su ma boye cewa sato kudin za su yi daga gwamnatocin jihohi su baiwa PDP ta yi yakin nemar zabe.

Tsohon gwamnan ya ce kamar yadda PDP ke yi haka ita ma APC ke yi saidai kawai APC din ba ta fito fili ta fada ba ne. Ya ce a matakin karamar hukuma ko a jiha ko a tarayya abin da ita ma za ta yi Kenan. Y ace duk wata jam’iyya mai rike da gwamnati abin da ta ke yi Kenan. Y ace mafita kawai it ace a sami canji a dimokaradiyyance.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG