Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam din Da Amurka Ta Jefa Afghanistan Yayi Sanadiyar Mutuwar 'Yan ISIS 36


Uwar Bama Bamai
Uwar Bama Bamai

Gwamnatin 'kasar Afghanistan tace 'kasurgumin Bam din nan da Amurka ta jefa a Afghanistan din jiya Alhamis yayi sanadiyyar mutuwar ‘Yan kungiyar IS 36 sannan ya ruguza wani babban wajen ajiye makamai.

Bayanin da ma’aikatar tsaron Afghanistan ta bayar yau juma’a yace ba’a rasa ran farar hula ko guda ba a harin. Bam din mai nauyin Kilogram 10,000 wanda ake kira da ”Uwar Bama Bamai” an jefa shine a kan sansanin ‘yan 'kungiyar ISIS da ke Kudu maso gabashin Gundumar Nangarhar ta Afghanistan jiya Alhamis.

Ofishin shugaban 'kasar Afghanistan Ashraf Ghani yace an gudanar da wannan hari ne da hadin gwiwar Jami’an tsaron Afhganistan . Haka kuma ya kara da cewa Dakarun Afghanistan na hada kai da rundunar Turai ta NATO domin 'karfafa ya'kin da ake da kungiyoyin ‘Yan tsagerun.

Tsohon shugaban 'kasar Afghanistan Hamid Karzai yayi Allah wadai da amfani da wannna katafaren Bam akan 'kasar Afghanistan.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG