Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam Ya Hallaka Mutane 11 A Kabul


Hadaddiyar Daular Larabawa ta tabbatar da kashe jami'an diflomasiyyarta biyar da aka yi jiya Talata a wani harin bam din da aka kai birnin Kandahar na kudancin Afghanistan.

Fashewar ta hallaka mutane akalla 11 tare da raunata wasu 16, wadanda akasari manyan jami'an gwamnati ne. Gwamnan Lardin Homayun Azizi da Jakadan Hadaddiyar Daular Larabawa a Kabul, Juma Mohammed al-Kaaba, su na cikin wadanda su ka ji raunuka.

"Babu wata hujja, bisa jinkai ko da'a ko addini, wajen kai harin bam da kuma kashe mutane masu niyyar taimakon wasu. Allah ya albarkaci shahidanmu ya kuma sa su cika da imani," a cewar Firaminista kuma Mataimakin Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawan, Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum a yau dinnan Laraba ta kafar Twitter.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Hadaddiyar Daular Larabawa ta fadi jiya Talata cewa Jakadanta ya je Kandahar ne wani aikin jinkai na taimakon marayu a Afhanistan da kuma bayar da sanarwar daukar nauyin karatun wasu.

Mai magana da yawun Fadar Shugaban kasa Haroon Chakhansuri ya gaya ma manema labarai a Kabul cewa an tura wata babbar tawaga karkashin jagorancin mai bayar da shawara kan tsaron kasa ta yi bincike kan wannan hari na ta'addanci.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG