Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bamabamai Sun Tashi a Garin Bamenda, Kasar Kamaru


Shugaban Kamaru, Paul Biya
Shugaban Kamaru, Paul Biya

A karo na uku cikin makonni uku bamabamai sun sake tashi a garin Bamenda dake jihar da ta fi yawan masu anfani da harshen inigilish wadanda wajen watanni tara ke nan suna nuna kin jininsu da gwamnatin kasar.

Kakakin gwamnantin kasar Kamaru Isa Ciroma Bakari shi ya bayyanawa manema labarai batun fashewar bamabamai a garin Bamenda fadar gwamnatin jihar arewa maso yammacin Kamaru da take anfani da harshen ingilishi wadda kuma ta dade tana adawa tare da nuna kin jinin gwamnatin Paul Biya.

Yayinda yake jawabi a birnin Yaounde fadar gwamnatin kasar Kamaru Bakari yana mai cewa "ba zamu taba yadda da irin wadannan 'yan ta'adda su dinga zuwa cikin kasarmu suna bata mana kasarmu ba...Dole ne mu jajirce wajen ganin cewa mun dakile irin wannan ta'addanci a kasarmu".

Harin na Bamenda ya jikata dakarun tsaro uku da aka garzaya dasu asibiti.

Gwamnan jihar Bamendan Adock Afrique shi ma ya nuna bakin cikinsa da aukuwar lamarin. Ya kira jama'ar jihar da su bi doka da oda kuma su lura kada su bata zamantakewar dake tsakaninsu da suka gadadaga iyaye da kakanni.

Gwamnan ya kara da bada tabbacin zasu gudanar da bincike kan lamarin domin zakulo bata garin.

Ga rahoton Awal Garba da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:42 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG