Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bamabamai Uku Sun Fashe A Birnin Austin Na Jihar Texas A Nan Amurka


'Yan sandan Austin dake binciken lamarin da ya auku

Bamabamai ukun da suka fashe a wurare daban daban sun auku ne a wuraren jinsunan da ba farar fata ba lamarin da ya sa 'yan sandan birnin na ganin akwai kiyayya

Jami’an ‘yan sandan birnin Austin a jihar Texas sunce akwai alaka tsakanin kunshin boma baman da aka ajiye a kofar gidajen Amurkawa bakaken fata biyu da kuma wanda aka ajiye a kofar wata mace ‘yar jinsin spaniya da ta manyanta.

Daya daga cikin boma boman ya kashe wani matashi dan shekaru goma sha bakwai jiya Litinin, yayinda na biyu ya jiwa wata mace ‘yar shekaru saba’in da biyar rauni.

Wani bom kuma da aka dana ya kashe wani bakin fata dan shekaru talatin da tara ranar biyu ga watan Maris.

Babban jami’in ‘yan sanda na birnin Austin Brian Manley ya fada jiya Litini cewa, “Ba zamu kawar da shakkun cewa, yana da alaka da kiyayya ba”. Yace yan sanda suna gudanar da bincike domin tantance dangantakar mutanen uku.

Masu bincike na gwamnatin tarayya suna taimakon ‘yan sanda.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG