Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bamu Tsorata Ba Game Da Sanarwar Ofishin Jakadancin Amurka A Najeriya – Mazauna Abuja


ABUJA: Tambarin Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya
ABUJA: Tambarin Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya

‘Yan kasuwa mazauna birinin tarayya Abuja na cigaba da tofa albarkacin bakinsu a game da gargadin da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya yi  kan yiyuwar  yan ta'adda su kai hare-hare a kan wurare kamar kasuwanni, ofis-ofis, wuraren Ibada da nishadi a birnin na Abuja.

Muryar Amurka ta ziyarci sananniyar gadar nan ta AYA da ke zama mahadin birnin da jihar nasarawa don jin ra’ayoyin mutane game da wannan gargadi da matakan da suke dauka wajen kare kansu, la’akari da yadda aka rasa rayuka da dama a shekarar 2014 sakamokon harin bam da aka kai tashar motar Nyanya.

Da dama dai, sun bayyana cewa ba su tsorata ba kan barazanan kai harin kuma tuni su ka ankara wajen daukar matakan kare kawunansu

Masanin al’amuran tsaro a Najeriya Yahuza Ahmad Getso ya shawarci yan kasar baki daya da su yi taka tsan-tsan game da bayanan da ke fitowa daga ofishoshin jakadancin kasashen ketare a kasar.

Tuni dai hukumomin tsaro a Najeriya suka sha alwashin daukar matakai na ganin cewar ba’a samu wani hari ba a Abuja da ma sauran jihohi dake da iyaka da babban birnin tarrayar kasar

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00

XS
SM
MD
LG