Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ban Ce A Yiwa 'Yan Adawa Kisan Kyankyaso Ba


Birnin Katsina
Birnin Katsina

Inji gwamnan jahar Katsina Ibrahim Shehu Shema

Duk wanda ya ga bidiyon gwamnan jahar Katsina Ibrahim Shehu Shema ya ji abun da ya fada kuma ya kara jaddawa karara, duk wanda ya ga bidiyon ya ji gwamnan ya na kwatanta abokan hamayyar siyasa da kyankyasun da ake samu a masai, sannan ya cewa magoya bayan shi su yi mu su kisan kyankyasu da kuma sauran wasu bayanai masu tayar da hankali, amma da babban editan Sashen Hausa na Muryar Amurka Aliyu Mustapha ya tinkari gwamnan da maganar da aka ga yayi a cikin bidiyon sai ya kada baki ya ce bai fada ba, shi da masu siyasar banga yake, kuma ya ce canza kalaman shi aka yi, kamar yadda za ku ji a cikin tattaunawar da suka yi:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00
Shiga Kai Tsaye

Bidiyon na gwamnan jahar Katsina Ibrahim Shehu Shema ya jawo cacar baki da maida martani daga jama'a da dama a ciki da wajen kasar Najeriya.

XS
SM
MD
LG