Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Banabancin Zaben Shugaban Amurka Na Wannan Shekarar da Na Baya


Gangamin zabe na Hillary Clinton

A firar da abokiyar aiki tayi da Malam Rafsanjani ya bayyana banbancin dake akwai a zaben bana da wadanda aka saba gani can baya.

Abun da ya fi nuna banbanci shi ne a karon farko mace ta fito tana takarar shugabancin kasar Amurka.

Rafsanjani yace mutane da dama suna ganin lokaci yayi da ya kamata a baiwa mace damar ta dane kujerar mulkin kasar.

A tattaunawar da ya dinga yi da mutanen kasar kusan dukansu sun ce suna bukatar wanda zai kawo zaman lafiya ya ci zaben. Basa son duk wanda zai tada hankalin mutane. Dalili ke nan da mutane zasu fito kwansu da kwarkwatarsu su kada kuri'a.

Mutanen kasar basa son wadanda zasu kawo rigingimu a ma zabesu sam. Yanzu zaman lafiya ne burinsu. Basa son yaki ko cin mutunci jama'a ko kuma barazanar korar baki dake zaune a kasar.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:21 0:00

XS
SM
MD
LG