Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bankin Al'umma Na Numan da Kamfanin Dangote Sun Shiga Takunsaka


Irin motocin kamfanin shuga na kamfanin Savanah dake taka mutane a Numan

Bankin al’uma na Bonghe a garin Numan dake jihar Adamawa ya yi barazanar kai kanfanin sarrafa suga na Savanah mallakar gamayyar kanfanonin Dangote gaban kuliya neman a biya shi diyyar naira miliyan biyar.

Takaddama sakanin bankin da kanfanin ya samo asli daga zanga-zangar da leburori masu sarar rake suka yin a nuna rashin amincewarsu da jinkirta biyansu kudin alawus na aikin rana-rana da kanfanin ke biya karshe kowace wata ta hanun bakin amma kuma ya kasa turawa bakin kudin .

Shugaba bankin Mr, Leonard Dan Nzadon ya ce kanfanin ya kasa cika nashi bangare na yarjejeniyar su na sai ya aike da kudi a asusunsa kana biya leburorin lamarin da yasa suka harzuka har ya kai ga lalata kaddarorin bankin. Yana mai zargin kanfanin sarrafa suga na Savanah mallakar gamayyar kanfanonin Dangote da bata ma banki suna da rage masa kima a idon masu hulda da shi.

A daya bangaren kuma leburorin kanfanin sun koka da irin mummunar yanayi da suke aiki a ciki inda kimani leburori biyar ke mutuwa a duk wata daga tattaki sakamakon cunkoso da ake samu a tirelolin da ke jigilar mutane sama da dari zuwa bakin aiki kamar yadda wani lebura da ya bukaci in sakaya sunansa ya shaida mani ta wayar selula. Korafin da babban Jami’in ma’aikatar kula da ma’aikata ta tarayya na jihar Adamawa Mal. Usman Dibal ya tabbatar da shi amma ya ki in nadi muryarsa.

Shi ma babban manajan kanfanin sarrafa suga na Savanah mallakar gamayyar kanfanoni Dangote Injiniya Ta’aziya Akila Todi ya ce bai da izinin Magana da ni kan wadannan korafe-korafe lokacin da na tuntube shi ya bada ba’asi.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG