Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Banky W, Adesua Sun Samu Karuwa


Banky W da Adesua (Hoto: Shafin Banky W na Instagram)
Banky W da Adesua (Hoto: Shafin Banky W na Instagram)

Ma’aurata kuma fitattun jarumai a masana'antar shirya fina-finai ta Nollywood da ke Najeriya, Olubankole Wellington, wanda aka fi sani da Banky W da matarsa Adesua Atomi- Wellington, sun haihu.

Banky W ne ya sanar da hakan a shafinsa na Instagram da yammacin ranar Litinin yana mai farin cikin cewa an haifa masa da namiji.

“My baby (matata) ta haihu kuma abin da muke ta addu’ar nema kenan.” Banky W ya rubuta a shafinsa na Instagram hade da hoton Adesua wacce ta fito a matarsa a fim din “The Wedding Party 1&2.”

A shekarar 2017 jaruman suka yi aure. Wannan shi ne dansu na farko.

Banky W da Adesua sun sha yin fim tare, baya ga “The Wedding Party” ma’auratan sun fito a fim din “Up North,” wanda aka yi a shekarar 2018.

Banky W a fim din "Up North" (Hoto: Shafin Instagram na Banky W)
Banky W a fim din "Up North" (Hoto: Shafin Instagram na Banky W)

Dan shekara 39, Banky kan yi waka baya ga fitowa da yake yi a fina-finan Nollywood.

Ya kuma taba tsayawa takarar majalisar dokokin Najeriya a shekarar 2019 inda ya nemi ya wakilci mazabar Iso Ota ta jihar Legas da ke kudancin Najeriya.

Baya ya ga fitowa a matsayin jaruma, Adesua kan yi aikin furodusa a dandalin hada fim din na Nollywood.

Tana kuma daya daga cikin jarumai mata da ake ji da su Nollywood.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG