Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wadanda Suka Sace Damishi Sango Sun Nemi Fansar Naira Miliyan 100


Mutanen da suka sace tsohon ministan wasanni na Najeriya, kuma shugaba mai ci na jam'iyyar PDP a Jihar Filato, Damishi Sango, sun bukaci da a biya su Naira miliyan dari kafin su sako shi tare da sauran mutane hudu da suka sace su jiya laraba da maraice.

Kakakin jam'iyyar PDP a Jihar Filato, Joseph Akansa, ya shaidawa wakiliyar VOA Hausa, Zainab Babaji, cewa barayin da suka sace tsohon ministan da wadanda suke tafiya tare, sun bar wata waya ta wani mukarrabinsa a cikin motar, wadda kuma ta wannan wayar suka sanar da jami'an tsaro irin bukatunsu.

An sace Damishi Sango tare da sauran mutanen a kusa da Jere a Jihar Kaduna, lokacin da suke kan hanyar zuwa Abuja daga Jos a bayan wani taron da suka yi game da babban taro na kasa na jam'iyyarsu da za a gudanar.

Ga cikakken bayanin sace mutanen da kuma irin matakan da suke dauka daga bakin kakakin jam'iyyar ta PDP a Jihar Filato, John Akans.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:57 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG