Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barcelona Na Zawarcin Dan Wasan Man City Angelino


Brcelona

A kasar Spain kuma kungiyar kwallon kafar Barcelona ta soma zawarcin dan wasan Manchester City ta Ingila Angelino, wanda ya dawo daga zaman aro na tsawon watanni 6 a kungiyar RB Leipzig ta kasar Jamus.

Angelino ya koma City ne a shekara ta 2014, inda ya bar ta a shekara ta 2018, amma ya sake komawa City din a bara.

Angelino
Angelino

Angelino dan kasar Spain mai shekaru 23, ya bugawa City wasanni 12 kafi wucewarsa Jamus a kakar wasanni da ta gabata.

City din na bukatar fam miliyan 27 ne daga Barcelona domin sayen dan wasan, kamar yadda tun farko ta baiwa Leipzig zabin sayen dan wasan.

Barcelona na kokarin yi garambawul ne na zubin ‘yan wasanta a karkashin sabon koci Ronald Koeman, biyo baya mummunan kashin da kungiyar ta sha daga Bayern Munich da ci 8-2, a wasan quarter-final na gasar zakarun Turai a makon da ya gabata.

Facebook Forum

Diego Maradona 1960-2020
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:07 0:00
Karin bayani akan Diego Maradona
XS
SM
MD
LG