Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bashar al-Assad Ya Kori Gwamnan Lardin Hama,inda Masu Zanga Zanga...


Magoya bayan shugaba Bashar al-Assad na Syria ne suke dauke da makeken tutar kasar a wata Zanga zanga ranar Jumma'a.

Shugaban Syria Bashar al-Assad ya kori gwamnan lardin Hama, inda jiya jumma’a dubun dubatan jama’a suka cika tituna suna kiran da a hambare shugaban kasar.

Shugaban Syria Bashar al-Assad ya kori gwamnan lardin Hama, inda jiya jumma’a dubun dubatan jama’a suka cika tituna suna kiran da a hambare shugaban kasar.

Kamfanin dillancin labaran Syria SANA ne ya bada snarwar haka yau Asabar, sai dai ba’a bada wani dalili na daukar wan nan mataki ba. A zanga zangar da aka yi jiya jumma’a, ‘yan gwagwarmaya sunce an kashe mutane goma sha hudu, a arangamomi da jami’an tsaro a fadin kasar.

Suka ce zanga zangar ta jiya ita ce mafi girma tun fara tutsun a watan uku.

A jiya jumma’an masu zanga zaga sun hallara kusa da kan iyakar kasar da Turkiyya, a sassan tsakiyar kasar, d a kuma wasu sassa na babban birnin kasar Damascus.

Yana da wuya a samu kafofi masu zaman kansu da zasu gaskanta sahihanci rahotanni daga Syria, domin 'yan jarida kalilan ne daga kasashen waje gwamnati ta baiwa izini shiga kasar, kuma su din ma ana takaita zirga zirgansu.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG