Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Batun Gudanar da Zabe Hakkin Hukumar Zabe ne ta {INEC}


Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, (INEC) Attahiru Jega
Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, (INEC) Attahiru Jega

Rundunar ‘yan Sanda jihar Adamawa, tace a shirye take don ganin an gudanar da zabe, a jihar baki daya wanda ya hada da sansanonin ‘yan kudun hijira .

A wani taron masu ruwa da tsaki da rundunar ‘yan Sanda jihar ta gudanar da shuwagabanin jam’iyu, a jihar, Kwamishinan ‘yan Sandan jihar Mr. Gabriel, yace “ Mun shirya don gudanar da zabe a arewacin jihar Adamawa da ake ta ce-ce ku-ce, kun san batun gudanar da zabe hakkin hukumar zabe ne ta {INEC} bana jami’an tsaro ba, mu namu shine mu bada kariya lokaci da ake zabe don haka a shirye muke.”

Wannan na zuwane yayin da Gwamna Jihar, Mr. James Bala Ngillari, ke ci gaba da nanata kiran da yake yin a da a dage zaben duk da yake ma shine jam’iyyar PDP, ta baiwa kujerar sanata, na mazabar Adamawa ta arewa.

Gwamnan, yace “ Na san wasu na sukata game da kiran da nayi na a dage zabe nifa ina kan bakata, aima bai kamata a gudanar da zabe ba, a wannan yanayi da ake ciki inda mutanen mu da dama ke gudun hijira, ai kamata yayi mu maida hankali wajen nuna alhini da tashin hakalin da ake ciki baiwa zabe ba.”

Siyasar Adamawa - 2'30"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:30 0:00

XS
SM
MD
LG