Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Baya Ga Rikicin Siyasa, Jahar Taraba Ta Kuma Shiga Rikicin Rashin Biyan Albashi


Gwamna Darius Ishaku na jahar Taraba

Yayin da jahar Taraba ke fuskantar karuwar rigingimun siyasa, sai ga shi kuma ta fada rigimar rashin biya albashi.

Yayin da jahar Taraba ke fama da kara tabarbarewar rikicin siyasa, ta kuma samu kanta cikin tabargazar rashin biyan albashin ma’aikata musamman ma na wasu kananan hukumomi na tsawon wata da watanni. Hasali ma, wasu na zargin an kuma zabtare masu albashi.

Wakilinmu a shiyyar Adamawa Ibrahim Abdul’aziz ya yi hira da wasu daga cikin ma’aikatan, wadanda su ka ce wasunsu na bin bashin watanni hudu. Su ka ce ba su kadai ba ne har ma da ma’aikatan wasu sassan irin na lafiya, da NUT da NULGE. Su ka ce a yanzu ma kafin a saka albashinsu a banki, bankin na bin asusun albashinsu bashin da ya fi albashin yawa.

Tuni kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomin (NULGE) Jahar Taraba ta yi gargadin cewa muddun aka cigaba da kin biyan mambobinta to ba za ta lamunta da hakan ba. Sakataren kungiyar ta NULGE a Jahar Taraba, kwamrad Garba Adamu ya yi takaicin abin da ya kira zabtare dan albashin ma’aikata da kananan hukumomi ke yi saboda sun ci bashin banki.

Ibrahim y ace ya yi kokarin jin ta bakin babban Sakataren Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Masarautun Jahar Alhaji Bello Yero don jin martanin gwamnatin jaha game da zargin cewa zabtare kudaden Kananan Hukumomi da gwamnatin jahar ke yi ke sa su kasa biyan albashin ma’aikatansu amma abin ya ci tura. To saidai mai bai wa Gwamnan Shawara kan Harkokin Siyasa Alhaji Abubakar Bawa, y ace zargin ba gaskiya ba ne. Ya ce kuma ba ma’aikata ba ne kawai gwamnatin jahar ke kula da sub a.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

XS
SM
MD
LG