Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayyana Sunayen 'Yan Takara Da Masu Zabe Ya Jawo Cece-kuce


Jami'an Hukumar Zabe ta INEC
Jami'an Hukumar Zabe ta INEC

Kamar yadda siyasa ta gada, bayyana sunayen 'yan takara ke da wuya sai aka shiga jayayya kan sunayen a wasu jahohin da su ka hada da Adamawa

Yanzu haka tuni hukumar zabe a Najeriya ta INEC,ta kammala baje sunayen masu kada kuri’a da kuma na yan takara domin shiga zaben shekarar 2019, da ke tafe. Sai dai kamar yadda siyasa ta gada, a wasu wuraren sunayen da aka baje sun janyo takaddama.

A jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya,har yan takara mata kusan takwas da kuma wani limamin jumma’a da kuma fasto ne suka tsaya takarar kujerar gwamna, batun da hukumar zaben ke cewa cigaba ne a demokaradiyya.

To sai dai kuma yayin da komi ke kankama a jihar Adamawa, a makwabciyar ta kuwa, jihar Taraba, har yanzu da sauran rina a kaba a jam’iyar APC , inda wasu kusoshin jam’iyar ke ficewa yayin da wasu ke kwanciyar likimo, bayan sabi-doran da ake zargin ya auku lokacin zabukan fidda gwani a jihar.

Ga dai wakilinmu na shiyyar Adamawa da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:08 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG