Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BBOG, Kungiyar dake Fafutikan An Sako 'Yan Matan Chibok Tayi Tattaki Zuwa Fadar Shugaban Kasa Muhammad Buhari

Tun lokacin da 'yan kungiyar Boko haram suka sace 'yan matan makarantar Sakandare dake Chibok ranar 14 ga watan Afirilun shekarar 2014 kungiyar BBOG, ko Bring Back Our Girls, ta shiga kan gaba wurin yin anfani da hanyoyi daban tana jawo hankalin gwamnati a sako 'yan matan

Jiya kungiyar BBOG, ko Bring Back Our Girls a turance, tayi maci inda tayi tattaki zuwa fadar shugaban Najeriya tana neman a sako sauran 'yan matan Chibok da har yanzu suke hannu 'yan Boko Haram.
Ita dai wannan kungiya ta sha yin zaman dirshan dare da rana akan fafutikar ganin an kubutar da 'yan matan Chibok. Hakansu ya cimma ruwa saboda an samu a kubutar da wasu . Duk da nasarar da aka samu kungiyar bata yi shiru ba. Har yanzu tana ci gaba da yin fafutika dalili ke nan da ta fito jiya tayi tattaki zuwa fadar shugaban kasar Najeriya dake Aso Rock ko kuma Aso Villa

Domin Kari

XS
SM
MD
LG