Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Benjamin Netanyahu Yace A Shirye Yake Yayi Sassauci Mai Zafi Domin Cimma Zaman Lafiya Da Falasdinawa


Benjamin Netanyahu yana jawabi gaban majalisar dokokin Amurka

Amma yace kasar bani Isra'ila ba zata janye zuwa bakin iyakokinta na 1967 ba, kuma ba zata saki ko inci guda na birnin Qudus ba

Firayim minista Benjamin Netanyahu na bani Isra’ila yace a shirye yake yayi sassauci mai zafi domin cimma zaman lafiya da Falasdinawa, amma kuma yace Isra’ila ba zata janye ta koma ga yadda bakin iyakokinta suke kafin yakin 1967 ba.

An yi ta mikewa ana jinjina wa Mr. Netanyahu jiya talata a lokacin da yayi jawabi a gaban zaman hadin guiwa na majalisun dokokin tarayyar Amurka biyu.

Yace rikicin Isra’ila da Falasdinawa ba wai rikici ne kan kafa kasar Falasdinu ba, rikici ne da ake yi a saboda Falasdinawa sun ki yarda su amince da kafuwar kasa ta yahudawa. Yace Isra’ila zata nuna dattaku wajen kamfatawa Falasdinawa kasa mai girma, amma kuma ya kara da cewa har abada ba za a raba birnin Qudus gida biyu ba.

Mr. Netanyahu yace za a iya cimma zaman lafiya ne kawai ta hanyar tattaunawa, ya kuma bayyana adawarsa da shirin da Falasdinawa ke yi na neman MDD ta amince da kasar Falasdinu a watan Satumba. Yace Isra’ila ba zata amince da gwamnatin Falasdinawa dake samun goyon bayan kungiyar Hamas ba, kungiyar da ya bayyana a zaman al-Qa’idar Falasdinawa. Har ila yau yayi gargadi game da kyale kasar Iran ta mallaki makaman nukiliya, yana mai fadin cewa duniya zata ganewa idanunta bala’in ta’addancin nukiliya idan har hakan ya faru.

XS
SM
MD
LG